Amurka ta saka sunan Shekau cikin jerin sunayen ‘Yan Ta’adda
Gwamnatin Amurka ta saka sunayen shugabannin Kungiyar Boko Haram a Najeriya cikin jerin sunayen ‘Yan Ta’adda tare da bayyana kungiyar ta kashe mutane sama da 1,000 a jerin haren haren da kungiyar ta yi ikirarin daukar nauyi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutane uku da aka saka sunansu sun hada da Abubakar Shekau da Abubakar Adam Kambar da Khalid Barnawi amma ba tare da saka suna kungiyar Boko Haram a jerin kungiyoyin ‘Yan Ta’adda ba na Duniya.
Gwamnatin Amurka ta ce Abubakar Shekau ne ta dauka matsayin shugaban Kungiyar Boko Hara amma Abubakar Adam Kambar da Khalid al-Barnawi suna da alaka ne da kungiyar Al Qaeda a reshen Maghreb.
Sanarwar daga Amurka tace Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai jerin hare hare da dama a Arewacin Najeirya karkashin jagorancin Abubakar Shekau.
A daya bangaren kuma rahotanni daga Najeriya sun ce Jami’an tsaro sun cafke Habibu Bama a Damaturu wanda ake zargin ya jagoranci kai harin ranar Kirsimeti da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 44.
Kafar Telebijin ta NTA a Najeriya ta tuwaito cewa an cafke Hsbibu Bama ne a garin Damaturu bayan musayar wuta da Jami’an tsaro
An dade Jami’an tsaro suna farautar Habibu Bama wanda ake zargin yana da hannun da harin da aka kai a ranar Kirsimeti a wata Coci a Madalla kusa da Abuja.
Gwamnatin Jahar Kaduna tace ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’I 24 bayan barkewar rikici a Jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu