Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashin shugabanci nagari ya sa Najeriya za ta mika kai ga Amurka-ACN

Jam’iyyar adawa ta ACN a Najeriya ta ce rashin shugabanci na gari ya sa Gwamnatin Najeriya za ta sadaukar da ‘yancinta ga Amurka wanda zai bata damar kai hari a cikin kasar, bayan sanya shugabannin kungiyar Jama’atu Ahlil Sunnah lida’awati wal Jihad (Boko Haram), a matsayin ‘Yan ta’adda.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan,
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

A wata sanarwa da kakakin ACN, Lai Muhammed ya sanyawa hannu, Jam’iyar tace wasikar da Jakadan Najeriya ya rubutawa Amurka, yana roko ya nuna gazawar gwamnatin Najeriya da rashin samun shugabanci na gari.

Tun bayan saka sunan su Shekau cikin Jerin sunayen ‘Yan ta’adda a duniya, kasar Amurka ta ce zata kaddamar da hare hare ga ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Jam’iyar adawa ta ACN ta bukaci Majalisar Najeriya, daukar matakin gaggawa don haramtawa Amurka sanya hannu game da al’amurran da suka shafi Najeriya ba tare da nuna banbancin Jam’iya ba.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace babu yadda za’a yi kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah lidda’awati wal Jihad da ake kira Boko Haram tare da masu goya musu baya su gurgunta ayyukan gwamnati. Shugaban ya fadi haka ne domin kare kansa daga zargin ya fice kasar zuwa taro a Brazil, lokacin da Kaduna da Yobe ke cin wuta.

“Boko Haram da masu daukar nauyinsu, ba zasu taba hana gwamnatinmu gudanar da ayyukan mu ba, zamu ci gaba da tafiye tafiyenmu, daga bangaren shari’a, zuwa bangaren gwamnati da daraktoci da manyan Sakatarori da Ministoci zuwa mataimakin shugaban kasa” inji Shugaba Goodluck Jonathan.

A cewar Shugaban rikicin Boko Haram ba zai dakile ayyukan gwamnati ba. Amma yana jajantawa kan ta’adin da ‘Yan kungiyar suka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.