Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojan Najeriya ya taka nakiya a Dajin Sambisa

Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar soja guda da wasu ‘yan kato da gora uku a dajin Sambisa a Jihar Borno, a lokacin da dakarun kasar suka nufi sansanin domin kakkabe mayakan Boko Haram.

Dakarun Najeriya da ke fada da Boko Haram a  Dajin Sambisa
Dakarun Najeriya da ke fada da Boko Haram a Dajin Sambisa Ben Shemang / RFI
Talla

Wasu majiyoyin tsaro daga Jihar Borno yankin arewa maso gabacin Najeriya sun shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa saboda fargaban binne nakiyoyi a dajin Sambisa, Dakarun kasar sun gagara kutsawa dajin.

Sai dai kakakin rundunar sojan, Manjo Janar Chris Olukolade ya fadi cewa Sojojin na iyakacin kokarin kakkabe ‘yan Boko Haram daga dajin, tare da tabbatar da mutuwar wani babba Soja.

Ana dai hasashen Mayakan Boko Haram na garkuwa ne da daliban makarantar Chibok sama da 200 da suka sace a watan Afrilun bara. Ko da ya ke wasu majiyoyi na cewa an fice da ‘yan matan zuwa Chadi da Kamaru.

Rahotanni sun ce bayan dakarun Chadi da Kamaru da Nijar da na Najeriya sun fatattaki Mayakan Boko Haram a Bama da Dikwa da Gwoza da Damboa yanzu sun dawo Dajin Sambisa.

Tuni kuma dakarun Najeriya suka ce sun kaddamar da farmaki a Sambisa, sansanin mayakan na karshe da ya rage a karbo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.