Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun kai hari dajin sambisa

Rahotannin sun ce, Sojojin Najeriya sun kai hari a dajin Sambisa, wurin da ake gani a matsayin maboya  kungiyar Boko Haram ta karshe. Kakakin rundunar sojin, Chris Olukolade, ya sanar da cewar sojin suna kai farmaki a dajin Sambisa, wanda ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya dake yaki da Boko Haram REUTERS/Tim Cocks
Talla

Gwamnatin Najeriya dai ta sha alwashin dakile hare-haren Mayakan da’a yanzu suka kai shekara 6 suna tada zaune tsaye

A baya dai Shugaba Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan ya sha alwashin kawo karshan kungiyar, kafin rantsar da shugaba mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari, a ranar 29 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.