Isa ga babban shafi
Nigeria

A Nigeria 'Yan Boko Haram Sun Kashe Mutane 12 a Gwoza

Wasu majiyoyin soja a Nigeria na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun yi wa wasu mutane 12 yankan rago a garin Gwoza na jihar Borno, yayin da sojoji ke kokarin kwashe fararen hula daga inda ake barin wuta.Majiyoyin sun shaidawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa garin Gwoza inda aka fatattaki ‘yan Boko Haram akwai sauran wasunsu da suka makale kuma anan ne aka sami wannan bakin labara.Rashin tabuka komi gameda lamarin ‘yan kungiyar Boko Haram na daga cikin abubuwan da suka sa Shugaba Goodluck Jonathan gaza samun nasarar zaben sa don ya zarce da mulki.  

Irin barna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi
Irin barna da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi AFP PHOTO/REINNIER KAZE
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.