Kamaru-Boko Haram
Boko Haram ta kashe mutane 10 a kamaru
Majiyoyin tsaro a kasar Kamaru sun ce mayakan Boko Haram sun kai hari a wasu garuruwa da ke yankin Kolofata da ke gab da iyakar da Najeriya inda suka kashe mutane akalla 10.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanin sunce, Maharan sun tsallaka kan iyaka zuwa cikin Najeriya, kafin sojojin Kamaru su iso.
Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin kasar da kuma na Chadi ke ci gaba da farautar mayakan kungiyar ta Boko Haram a yankin.
Kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a arewacin Kamaru da Chadi da kuma Nijar, amma mafi yawancin hare-harenta a Najeriya ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu