Isa ga babban shafi
Najeriya

Mata 2,000 Boko Haram ta sace, inji Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International tace akalla mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon shekarar da ta gabata, a yayin da a yau Najeriya ke juyayin cika shekara guda da sace ‘Yan mata 219 daliban Makarantar garin Chibok, da ke cikin Jihar Borno.

Gangamin masu fafatikar ganin an kubutar da 'Yan Matan Chibok da Boko Haram ta sace a Najeriya
Gangamin masu fafatikar ganin an kubutar da 'Yan Matan Chibok da Boko Haram ta sace a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kungiyar tace mayakan Boko Haram suna lalata da wasu ‘yan matan, tare da tursasa mu su daukar makamai.

Kungiyar tace Boko Haram na garkuwa ne da matanan a dajin Sambisa, wasu kuma ana garkuwa da su ne a  tsaunin Gorsi da ke gabar ruwan tabkin Chadi a cikin Kamaru.

Rahoton na Kungiyar Amnesty ya ce kusan mutane 200, da suka hada da mata da ‘yan mata 28, da suka tsere daga hannun mayakan, sun bayar da bahasi, inda suka ce su aikinsu shi ne su yi harbi su yanka mutane ko su kashe su.

Kungiyar ta kuma bayyana yadda ake shigar da maza da yara kanana cikin kungiyar da karfin tsiya ko a kashe su, yayin da ake kame mata a yi ma su fyade, tare da musu auren tilas.

Kame ‘yan matan Chibok su 280, da aka yi ya ja hankulan al’ummar duniya, tare da tallafin kungiyar nan ta #BringBackOurGirls.

An dade rundunar Sojin Najeriya na ikirarin cewa ta san inda ake garkuwa da ‘Yan matan Chibok, amma sun bayyana fargaba akan tsoron kada a kashe su wajen kubutar da su.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo yana ikirarin cewa ya aurar da dukkanin matan tare da musuluntar da su.

Amma a cikin rahoton da Amnesty ta fitar, wata yarinya da ta tsere da aka zanta da ita tace mayakan sun yi ma ta Fyade sau da dama, wani lokaci taron dangi su ke yi.

Amnesty tace tana son a kaddamar da binciken laifukan yaki da mayakan Boko haram suka aikata, yayin da rahoton kungiyar ya kiyasta cewa sama da mutane 4000 suka mutu a 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.