Chibok: Malala ta kawo ziyara a Najeriya
Malala Yousafzai, Dalibar kasar Pakistan da Mayakan Taliban suka harba akan gwagwarmayar da take yi na ilimin ‘yaya mata ta kawo ziyara a Najeriya, inda ta gana da wasu iyayyen ‘Yan matan da mayakan Boko haram suka sace sama da 200 a garin Chibok.
Wallafawa ranar:
A gobe litinin ne ake sa ran Malala, zata gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a dai dai lokacin da aka shafe watanni uku da sace ‘Yan mata kimanin 276 a garin Chibok a cikin Jahar Borno.
Dalibar kuma ta gana da kungiyoyin da ke fafutikar ganin an sako ‘Yan matan a Najeriya tare da yin kira ga gwamnatin Najeriya ta hanzarta wajen ganin an kubutar da ‘Yan matan da aka sace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu