Isa ga babban shafi

Emefiele ya kashe biliyan 18 wajen buga takardun kudi na naira miliyan 685- EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta bankado yadda tsohon gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele ya kashe kudin da yawansu ya kai Naira biliyan 18 da miliyan 960 wajen buga takardun kudin naira miliyan 684 da dubu 590.

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele.
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Duk da yadda aikin buga sabbin takardun kudin da Emefiele ya jagoranta ya gudana neb isa sahalewar shugaban kasar na wancan lokaci Muhammadu Buhari, lamarin ya gamu da kakkausar suka baya ga jefa miliyoyin ‘yan Najeriya a halin kakanikayi.

Emefiele wanda ke fuskantar tuhuma kan zarge-zargen badakalar rashawa da almundahanar kudade, a sabbin tuhume-tuhume 4 da yanzu haka ya ke fuskanta gaban babbar kotun kasar har da yin gaban kansa wajen aiwatar da dokar da ta azabtar da al’ummar Najeriya.

Babbar Kotun ta Najeriya ta tuhumi Emefiele da barnatar da kudade karkashin tsarin sauya fasalin takardun kudin Naira 200 da 500 da kuma 1000 da ya jagoranta a gab da karkarewar mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari.

A ranar 30 ga watan da muke ciki ne Godwin Emefiele zai sake gurfana gaban kotun da ke birnin Abuja fadar gwamnatin Najeriya don amsa sabbin tuhume-tuhumen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.