Isa ga babban shafi

Kungiyar kwadagon Najeriya za tayi zaman dirshan a bankin CBN

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta umurci dukkan ma’aikata da su fara mamaye dukkanin rassan ofisoshin babban bankin Najeriya a fadin kasar daga mako mai zuwa, kan matsalar karancin takardun kudi da ake fama da ita a kasar.

Shugabannin gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC yayin tattakin zanga zangar adawada gwamnati a birnin Abuja
Shugabannin gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC yayin tattakin zanga zangar adawada gwamnati a birnin Abuja REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ne ya bayar da umarnin, yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abuja.

Wannan na zuwa ne, bayan umarnin da kungiyar kwadagon ta bawa mambobinta da ke aiki a bankuna, da su tsunduma yajin aiki.

Ya ce umarnin ya zama wajibi ne biyo bayan cikar wa’adin mako guda da aka ba wa babban bankin na ys samar da tsabar kudi ga ‘yan Najeriya.

Rashin isassun takardun kudi ya jefa al’ummar Najeriya da dama cikin mummunan yanayi, yayin da ‘yan kasuwa ke ci gaba da koka wa da kuma kira ga gwamnati, da ta kawo musu daukin gaggawa.

Biyo bayan furucin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi na cewa bai nemi babban bankin Najeriya CBN da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya da su bijirewa umarnin kotun koli ba, babban bankin ya bayyana cewa za a iya ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, 500 da kuma 1,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.