Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ba ta bukatar taimakon Sojin MDD-Jonathan

Shugaba mai barin gado a Najeriya Goodluck Jonathan ya ce kasarsa ba ta bukatar Majalaisar Dinkin Duniya ta aiko da dakarunta domin taimakawa wajen yaki da Boko Haram.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron Afrika kan sha'anin tsaro a Kenya.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a taron Afrika kan sha'anin tsaro a Kenya. REUTERS
Talla

Shugaban ya ce kamata ya yi Majalisar ta mayar da hankali wajen bayar da tallafi domin sake gina al’ummar da rikicin ya shafa.

Jonathan ya fadi haka ne bayan ya gana da wakilai majalisar na musamman a yammaci da tsakiyar Afrika, Mohammed Ibn Chambas da Abdoulaye Bathily.

Jonathan ya ce taimakon da suka samu daga makwabta Nijar da Kamaru da Chadi ya sa sun samu nasarar karbo garuruwa da dama da mayakan Boko Haram suka kwace.

Hukumar ‘yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin Boko Haram ya raba mutane sama da miliyan guda da rabi da gidajensu, yayin da aka kashe mutane sama da 13,000.

Chambars ya ce ya kawo ziyara ne a kasashen da rikicin Boko Haram ya shafa, tare da jaddada cewa Majalisar Dinkin Duniya a shirye ta ke ta taimakawa Najeriya da makwabtanta domin kakkabe ayyukan Boko Haram.

A cikin jawabinsa, Jonathan wanda ya sha kaye a zaben shugaban kasa ya yi kira ga kasashen duniya su taimakawa gwamnatin Janar Muhammadu Buhari wajen yaki da ta’addanci.

Chambers ya yaba da yadda Jonathan ya amince da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga Maris.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.