Isa ga babban shafi
Najeriya

Iyayen matan Chibok na cikin damuwa

14 ga watan Fabrairu aka cika shekara guda da mayakan Boko Haram suka sace ‘Yan mata Daliban Makaranta su 276 a garin Chibok Jihar Borno arewacin Najeriya. Kungiyoyi da dama sun hada gangami a Najeriya domin yin kira ga hukumomin kasar su gaggauta kubutar da ‘Yan matan.

Iyayen Matan garin Chibok da Boko Haram ta sace
Iyayen Matan garin Chibok da Boko Haram ta sace RFI hausa/Bilyaminu
Talla

A ranar cika shekara guda a jiya Talata Iyayen matan na Chibok sun hada gangami a makarantar da aka sace ‘yayansu domin jimami.

Wakilin RFI Hausa Bilyaminu Yusuf ya yi tattaki zuwa garin Chibok kma ya iske iyayaen matan sun taru sun kuka.

03:21

Rahoton Bilyaminu Yusuf daga Chibok

RFI

Wata daga cikin iyayen day a zanta da ita, tace kullum tana mafarkin an kashe ‘yarta, amma tana bukatar ta yi tozali da gawar.

A ranar 14 ga watan Fabrairun bara ne mayakan Boko Haram suka abka wa makarantar mata a garin Chibok cikin Jihar Borno suka sace ‘Yan mata 276 a lokacin da suke shirin rubuta jarabawa.

57 daga cikin matan sun tsere amma har yanzu babu wani labari game da sauran ‘yan matan.

Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi alkawalin kubutar da ‘Yan Matan ba saboda har yanzu ba a san inda ake garkuwa da su ba.

Amma a cikin sanarwar da ya fitar, Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi iya kokarinta domin mika ‘Yan matan ga iyayensu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta wallafa rahoto da ke cewa akalla mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon shekarar da ta gabata.

Amnesty tace mayakan Boko Haram suna lalata da wasu ‘yan matan, tare da tursasa mu su daukar makamai.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo yana ikirarin cewa ya aurar da dukkanin matan tare da musuluntar da su.

Kame ‘yan matan Chibok su kusan 280, da aka yi ya ja hankulan al’ummar duniya,.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.