Isa ga babban shafi
Wasanni

An bai wa Rooney jan kati a karawar Man United da West Ham

A karshen makon da ya gabata an buga wasanni da dama musamman ma a wasannin Lig na kasashen Turai, kuma daya daga wasannin da suka fi daukar hankulan jama’a ita ce karawar da aka yi tsakanin Man United da kuma West Ham inda aka bai wa keftin din Man U Wayne Rooney jan kati. 

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney
Dan wasan Manchester United Wayne Rooney REUTERS/Phil Noble
Talla

An dai bai wa Rooney jan kati ne ana sauran mintuna 30 a tashi wasan sakamakon yadda ya rugo a guje ya rafke dan wasan West Ham mai suna Stewart Downing, to amma duk da haka Kulob dinsa na Man United ya yi nasara a karar ci 2-1.

Rooney ya ce ba zai daukaka kara a game da wannan mataki da alkalin wasan mai suna Lee Mason ya dauka ba, to amma ya nemi afuwa daga masoya kulob dinsa na Man U.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.