Isa ga babban shafi
Ingila

Rooney yana son zama Kaftin na Manchester

Dan wasan Ingila Wyne Rooney yace yana son zama jagoran kungiyar Manchester idan har sabon kocin kungiyar Luis Van Gal zai ba shi dama kamar yadda Dan wasan ke shaidawa kafafin yada labaran Birtaniya. Sai dai kuma ana hasashen Robin Van Persie ne zai gaji Vidic wanda ya fice zuwa Inter Milan.

Wayne Rooney na Manchester United
Wayne Rooney na Manchester United REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Van Gal wanda a yanzu haka shi ne mai horar da ‘Yan wasan kasar Netherland, ya karbi aikin Manchester ne bayan kammala kakar wasa. Ana ganin Van Perise ya fi kusa da sabon kocin na Manchester saboda ko a Netherland Dan wasan ne ya ba Kaftin.

A game da gasar cin kofin duniya da za’a fara a Brazil, Wayne Rooney yace a bana zai taka rawar gani domin yana cikin koshin lafiya. A shekarun da suka gabata Rooney ya yi fama da rauni a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Jamus a 2006 da kuma Afrika ta kudu a 2010.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.