Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Jamus ta dauki kofin duniya na mata 'yan kasa da shekaru 20

A daren jiya aka buga wasan karshe na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 20, inda kasar Jamus ta sami nasarar sake daukar kofin, bayan ta yi wa Nigeria ci 1 da 0. An yi wasan a garin Montreal na kasar Canada.Sai da aka kara lokacin wasan kafin aka sami wanda ya yi nasara, kuma ‘yan matan na Nigeria sun taka leda sosai, inda suka yi kokarin daukar fansar cin da Jamusawan suka musu a wasan karshen gasar da aka aka yi shekaru 4 da suka gabata.A zagayen farko na wasan, ‘yan matan na Nigeria sun hana Jamusawan sakat, inda suka yi ta kai kora, a zagaye na 2 na gasar ma bata sake zane ba, don sun nunawa wa turawan kwarewa, amma sai mai tsaron gidan Jamusawan tayi ta karewa harin.Bayan da aka kara lokacin wasa sai Lena Petermann ta fidda Jamusawan kunya da kwallo daya tilo, da ta jefa a ragar ‘yan Nigeria.  

Alamar gasar cin kofin duniya na mata 'yan kasa da shekaru 20
Alamar gasar cin kofin duniya na mata 'yan kasa da shekaru 20 FIFA TM ©
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.