Isa ga babban shafi
Fransa

Tsaura matakan tsaro bayan Kashe Herve Gourdel

Bayan kammala taron Majalisar Tsaron Kasa a Faransa, a yanzu hukumomi sun bukaci a kara tsaurara matakan tsaro domin kare Faransawa da kuma kadarorinsu a ciki da wajen kasar.

Jami'in tsaro a Paris
Jami'in tsaro a Paris AFP /Lionel Bonaventure
Talla

Shugaba Francois Hollande ya bayyana cewa sakamakon kisan da aka yi wa Bafaranshe Herve Gourdel a Aljeriya, ya zama wajibi kasar ta kare al’ummarta daga barazanar ‘yan ta’adda.

An dai samu halartar manyan jami’ai da ke da ruwa da tsakani a lamarin tsaron kasar a wannan taro da ya gudana karkashin jagorancin shugaba Hollande, da suka hada da ministan cikin gida, na tsaro, babban kwamandan askarawan kasa da kuma jami’an hukumar tara bayanan sirri ta kasar DGSE.

A kowace shekara akwai Faransawa fiye da milyan 13 da ke kai ziyara a sassa daban daban na duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.