Isa ga babban shafi

Al'ummar Turkiya na zaɓen ƙananan hukumomi

Ƴan kasar Turkiya na kada kuri'a a zaben kananan hukumomi wannan Lahadi, inda shugaba kasar Recep Tayyip Erdogan ke neman kwato iko da birnin Istanbul daga hannun abokin hamayyarsa Ekrem Imamoglu,wanda ke da nufin tabbatar da 'yan adawa farin jininsa da karfin siyasa bayan da ya sha kaye a zaben bara.

Mutane na kaɗa kuri'u a wata rumfar zabe yayin zaben kananan hukumomi a birnin Istanbul na kasar Turkiyya 31 ga Maris, 2024
Mutane na kaɗa kuri'u a wata rumfar zabe yayin zaben kananan hukumomi a birnin Istanbul na kasar Turkiyya 31 ga Maris, 2024 © Dilara Senkaya / Reuters
Talla

Magajin garin Istanbul Imamoglu ya yi wa Erdogan da jam'iyyarsa ta AK duka mafi girma cikin shekaru 20, bayan nasara a zaben 2019, sai dai shugaban ya farfado a zaben shekarar 2023 ta hanyar tabbatar tazarcensa a shugabancin ƙasar da kuma rinjayen majalisar dokoki tare da abokan ƙawancensa masu kishin kasa.

Zakaran gwajin dafi

Sakamakon zaben na ranar Lahadi na matsayin zakaran gwajin dafi ga Erdogon da abokin hamayyarsa Imamoglu a kasar da ke zama mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO. Ana ganin nasarar Imamoglu wajen ci gaba da zama a kujerar magajin garin Instanbul ya kara tabbatar da burinsa na zama shugaban kasa nan gaba.

Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan na jawabiga magoya bayan jam'iyyarsa gabanin zaben kananan hukumomi a Istanbul, 29/03/24
Shugaban kasar Turkiya Tayyip Erdogan na jawabiga magoya bayan jam'iyyarsa gabanin zaben kananan hukumomi a Istanbul, 29/03/24 REUTERS - Umit Bektas

An bude rumfunan zabe da karfe 7 na safe wato 4 agogon GMT a gabashin Turkiyya da kuma wasu wurare da karfe 8 na safe, inda ake tsammanin sama da mutane miliyan 61 da suka yi rajistar su kada kuri'unsu.

Da karfe 5 ake rufe rumfunan zabe, kuma ana sa ran sakamakon farko da karfe 10 na dare.

A birnin Istanbul mai mutane miliyan 16 da ke tafiyar da tattalin arzikin kasar Turkiyya, kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa, za’a yi Imamoglu zai fuskantar kalubale daga dan takarar jam'iyyar AKP, Murat Kurum, wanda tsohon minista ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.