Isa ga babban shafi

Manyan kasashe sun fara aikewa Erdogan sakon taya murnar lashe zaben Turkiya

Kasashen Duniya na ci gaba da aike sakon taya murna ga shugaba Recep Tayyib Erdogan dangane da nasarar da ya samu wajen lashe zagaye na biyu na zaben Turkiya a jiya lahadi, wanda zai ba shi damar dorawa kan shekaru 20 da ya shafe ya na mulkar kasar.

Shugaba Recep Tayyib Erdogan yayin jawabi gaban magoya baya.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan yayin jawabi gaban magoya baya. © UMIT BEKTAS / REUTERS
Talla

Wannan ne dai karon farko da Turkiya ke zuwa zagaye na biyu a zaben shugaban kasa, bayan da shugaba Erdogan ya gaza kawo kashi 50 na kuri’un da aka kada makwanni 2 da suka gabata, duk da cewa shi ke da mafi yawan kuri’un da aka kada a tsakanin ‘yan takarar na wancan lokaci.

Shugabannin farko-farko da suka aikewa Erdogan sakon taya murna akwai Vladimir Putin na Rasha da ke matsayin abokin shugaban na Turkiya wanda ya bayyana nasarar a matsayin tagomashin jajircewarsa ga al’ummarsa, yayinda Joe Biden na Amurka ya yi fatan aiki tare da Erdogan ba tare da ambato takun-sakar da ke tsakaninsu a baya-bayan nan game da kungiyar tsaro ta NATO ba.

Sauran shugabannin da suka aike da sakon taya murnar ga Erdogan sun hada da Ursula von der Leyen ta kungiyar Tarayyar Turai kana Jens Stoltenberg na NATO sai kuma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress tukuna shugaba Emmanuel Macron na Faransa sannan Volodymyr Zelensky na Ukraine wanda ya yi fatan taimakawar Erdogan wajen dawo da zaman lafiya a nahiyar Turai, kana shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz wanda ya bayyana Turkiya a matsayin kawa ta kurkusa ga Jamus tare da fatan aiki tare a lamurran da suka shafi tattalin arziki da cinikayya.

Nasarar ta Erdogan dai na nuna cewa jagoran mai shekaru 69 zai ci gaba da jan ragamar Turkiyya har zuwa shekarar 2028 inda cikin jawabinsa na farko bayan sanar da sakamakon zaben, shugaban wanda ya shafe shekaru 20 yana mulkar kasar ya yi fatan aiki tare da bangarorin adawa don saka daga likafar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.