Isa ga babban shafi
Faransa

Ciyar da musulmi naman alade a gidajen yarin Faransa

A ja-in-jar shara’a kan ma’anar jamhuriyar da ba ruwanta da addini, kotun Fransa ta soke hukumcin da wata kotu ta zartas a cikin watan Nowambar bara, kan wani gidan yarin kasar da ya bukaci a bai wa fursunoni musulmi abincin halal a zamansu na yari.

Gidan yarin Val-de-Reuil fica a Faransa.
Gidan yarin Val-de-Reuil fica a Faransa. Ministério da Justiça da França
Talla

Gwamnatin kasar ta Fransa ce ta nemi jirkita hukumcin da wata kotun harkokin aiki ta zartas, da ya bukaci gidan yarin Saint-Quentin-Fallavier, da ke kudancin kasar ya dinga ciyar da fursunoni musulmi ta hanyar da tsarin addininsu ya tanada

Sai dai kuma a wannan talata wata kotun da ke birnin Lyon ta soke wannan hukumci da wacan kotun ta zartar, da cewa gidan yarin ya daina ciyar da fursunoinin musulmi naman Aladai ta hanyar ba su abinci da ya shafi ganyen itace ko kuma wasu nau’ukan abinci na musamman da ba haramun ba a tsarin addininsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.