Isa ga babban shafi

Guardiola ya ja layi kan korafin rashin amfani da Grealish a wasannin City

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya ce Jack Grealish zai iya dawowa cikin rukunin ‘yan wasan kungiyar ajin farko da za a rika amfani da su a kowanne wasa idan har kwazonsa ya dawo kamar yadda aka sanshi.

Wasanni 19 kadai Guardiola ya faro da Grealish a wannan kaka.
Wasanni 19 kadai Guardiola ya faro da Grealish a wannan kaka. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekaru 28, ya dokawa City wasanni 41 wadanda dukkaninsu aka faro da shi a kakar da ta gabata, tare da taimakawa kungiyar lashe kofuna 3 da suka Firimiya, FA da kuma Zakarun Turai.

Sai dai a wannan kaka wasanni 19 kadai Guardiola ya faro da shi da suka kunshi na Firimiya 7, lamarin da ke nuna farraka tsakanin dan wasan da kocin.

A cewar Guardiola ko shakka babu idan Grealish ya dawo da kwazo, a shirye ya ke ya mayar da shi cikin tawagar farko da ke shiga kowanne wasa na City.

Yayin tattaunawarsa da manema labarai Guardiola wanda ya yi kaurin suna wajen ajje zakakuran ‘yan wasa a benci da zarar salon wasansu ya fara sauyawa ko kuma tasu bata zo daya ba, ya ce salon wasan Grealish ya nan yadda ya ke sai dai kwazonsa ya matukar raguwa.

Har zuwa yanzu dai ba a ga kafar Jack Grealish a farkon wani wasa mai muhimmanci da City ta doka ba, domin kuwa Guardiola ya doka wasanni 4 ne a Community Shield da shi sai kuma wasannin European Super Cup da na Club World cup.

Hatta a wasannin Firimiyar da aka faro da shi anga yadda Guardiola ya sauya shi da Oscar Bobb a wasan da City ta yi nasara kan Sheffield United.

Dan wasan mai darajar fam miliyan 100 na ci gaba da zaman benci domin kuwa ko a nasarar City kan Bournemouth an ga yadda ya kare a gefe, kuma babu tabbacin ya iya faro wasan FA da za su kara da Luton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.