Isa ga babban shafi

Manchester za ta rabu da 'yan wasa 11 ciki har da Casemiro da Maguire

Wasu bayanai na nuna cewa dan wasan tsakiyar Brazil da ke taka leda da Manchester United Casemiro da takwaransa na Ingila Harry Maguire na cikin ‘yan wasa 11 da kungiyar ke shirin raba gari da su a karshen wannan kaka.

Ratcliffe preparing summer overhaul at Man United - sources
Ratcliffe preparing summer overhaul at Man United - sources © Sky Sports
Talla

Rahotanni sun ce matakin raba gari da tarin ‘yan wasan na zuwa ne bayan bukatar hakan daga Sir Jim Ratcliffe wanda ke da mallakin kashi 25 na kungiyar.

Bayan wata doguwar ganawa tsakanin Ratcliffe da Sir Dave Brailsford ne suka cimma jituwar rage yawan ‘yan wasan don karkata hankali kan zubin sabbin ‘yan wasan da za su kawowa kungiyar kudi hade da nasara.

A cewar Ratcliffe United na da kudaden da za ta iya hada-hada da su wajen kawo duk ‘yan wasan da ta ke so a kaka mai zuwa, amma kokarin kaucewa taka doka zai tilasta mata sallamar da ‘yan wasan 11 don musayarsu da wasu.

Lokacin da United ta samu kudi mafi yawa a tarihi dai shi ne a shekarar 2009 lokacin da ta sayarwa Real Madrid Cristiano Ronaldo a matsayin dan wasa mafi tsada a wancan lokaci.

Sai dai Ratcliffe na ganin idan har kungiyar ta iya sayar da ‘yan wasan 11 za ta rage kashe kudi da kuma fadada kasafinta bayan samun ‘yan canjin sayar da su.

To wadannan ‘yan wasa dai kamar yadda jaridar wasanni ta Spaniya ta ruwaito sun kunshi Christian Eriksen da Raphael Varane kana Casemiro da Maguire sai Scott McTominay da Aaron Wan-Bissaka sai kuma Victor Lindelof.

Sauran sun kunshi Anthony Martial wanda kwantiraginsa ke shirin karewa a karshen kaka, lamarin da zai bashi damar tafiya a kyauta yayinda kungiyar za kuma ta bayar da aron Jadon Sancho da Donny van de Beek da kuma Facundo Pellistri da Brandon Williams.

Sabon mai rike da ragamar ta Manchester United Sir Ratcliffe ya ce kungiyar za ta sayi sabbin matasa kuma zakakuran ‘yan wasa da suka kunshi masu cin kwallo da kuma masu tsaron gida, sai dai duk da hakan zai duba yiwuwar ci gaba da tafiya da Manaja Erik tem Hag zuwa karshen kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.