Isa ga babban shafi

Ratcliffe ya karbi ragamar tafiyar da sabogin kwallon kafa a Manchester United

An cimma yarjejeniyar sayar wa da hamshakin attajirin kasar Ingila din nan, Sir Jim Ratcliffe kashi 27 da dig 7 na hannun jarin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, inda aka yi kiyasin cewa jarinsa a kungiyar ya kai fam biliyan 1 da miliyan 25.

Hamshakin attajirin Birtaniya, Jim Ratcliffe.
Hamshakin attajirin Birtaniya, Jim Ratcliffe. © AFP / VALERY HACHE
Talla

Iyalan gidan Glazer, wadanda su ne masu wannan kungiyar tun a shekarar 2005, za su ci gaba da kasancewa masu hannun jari mafi yawa, amma kamfanin Ratcliffe, wato Ineos ne zai tafiyar da duk wata harka da ta shafi kwallon kafa.

Ratcliffe ya bayyana jin dadinsa a game da cimma wannan yarjejeniya, yana mai cewa abin alfahari ne kasancewa mamallakin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Ratcliffe wanda aka Haifa a birnin Manchester, shi ne shugaban kamfanin sarrafa albarkatun danyen mai na Ineos, kuma ya ce shi magoyinn bayan United ne.

Ya yi yunkurin sayen Chelsea a shekarar 2022, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.