Isa ga babban shafi

Liverpool ta lashe kofin Carabao karo na 10 bayan doke Chelsea

Liverpool ta lashe kofin Carabao bayan doke Chelsea da kwallo 1 mai ban haushi, kwallon da kyaftin Virgil van Dijk ya zura a karin lokaci, bayan da bangarorin biyu suka shafe ilahirin lokacin wasan ba tare da zura kwallo ba, kwatankwacin yadda suka yi a 2022.

Tawagar kwallon kafa ta Liverpool bayan lashe kofin Carabao karo na 10 a wasan da ta doke Chelsea da kwallo 1 mai ban haushi.
Tawagar kwallon kafa ta Liverpool bayan lashe kofin Carabao karo na 10 a wasan da ta doke Chelsea da kwallo 1 mai ban haushi. © FMM/RFI
Talla

Kofin wanda ke matsayin karo na 10 da Liverpool ke lashewa na zuwa ne duk da yadda ta doka wasan ba tare da zakakuran ‘yan wasanta ba, musamman bangaren masu cin kwallo da suka kunshi Mohamed Salah da Darwin Nunez da kuma Diago Jota wadanda dukkaninsu ke jinyar rauni.

Haka zalika ana tsaka da karawar ta jiya aka yi waje da Grabenberch lamarin da ya sake karya gwiwar Liverpool game da yiwuwar nasara a wasan.

Bugu da kari VAR ta soke kwallon van Dijk ta farko da aka bayyana da satar fage, gabanin kwallon da ya zura a minti na 118 da taimakon Kostas Tsimikas wanda ya yi bugun kusurwa.

Lashe kofin na Carabao ya zama babbar nasara ga Jurgen Klopp wanda ke jagorantar Liverpool a kaka ta karshe matsayin manaja, lura da yadda zai raba gari da kungiyar a karshen wannan kaka.

Carabao na matsayin kofi 1 cikin 4 da Liverpool ke hari a wannan kaka, ciki har da Firimiya da ta ke jagoranci yanzu haka sai FA da ta kai zagaye na 4 da kuma Europa.

A bangaren Chelsea rashin nasarar babbar koma baya ce ga Mauricio Pochettino da ke fatan daidaita kungiyar, haka zalika wasan na jiya ya zama karo na 6 da Chelsea ke shan kaye a Wembley ciki har da 3 a hannun Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.