Isa ga babban shafi

Arsenal ta sha duka a hannun Porto da kwallo 1 mai ban haushi

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta doka wasanta na jiyan da kafar hadu bayan shan duka da kwallo 1 mai ban haushi a hannun Porto, sai dai horarwa Mikel Arteta ya ce ko shakka babu tawagar ta shi za ta yi gyara a kura-kuren da suka kai ta ga shan kayen.

A watan gobe bangarorin biyu za su hadu a zagaye na biyu na rukunin na 'yan 16.
A watan gobe bangarorin biyu za su hadu a zagaye na biyu na rukunin na 'yan 16. Action Images via Reuters - PETER CZIBORRA
Talla

A karin lokaci ne ana minti na 94 gab da tashi daga wasa Porto ta zura kwallon a ragar Arsenal wanda ya bata damar samun rinjaye a haduwar farko, ko da ya ke sai a watan gobe ne za a tabbatar da wadda za ta tsallaka mataki na gaba a tsakanin manyan tawagogin biyu na Ingila da Portugal.

Arteta a zantawarsa da manema labarai bayan shan kaye a wasan na jiya ya ce ‘yan wasan na shi za su sauya sakamakon idan Porto ta yi tattakin zuwa arewacin London a watan gobe.

Wannan ne dai karon farko da Arsenal ke samun damar taka leda a rukunin ‘yan 16 na gasar ta cin kofin zakarun turai tun bayan kakar wasa ta 2010, haka zalika wannan ne karon farko da ta ke haskawa a gasar tun bayan 2017.

A cewar Arteta magoya bayan Arsenal za su kwazon tawagar a haduwar watan gobe domin kuwa za su iyakar kokarinsu wajen ganin basu baiwa magoya baya kunya ba.

Shi kansa tauraron dan wasan da Arsenal tas iya matsayin mafi tsada Declan Rice ya bayyana cewa zasu yi amfani damar kasancewarsu a gida wajen doke Porto a watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.