Crystal Palace ta nada tsohon kocin Frankfurt a matsayin sabon kocinta
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace da ke wasa a gasar Firmiya Ingila ta nada tsohon kocin Eintracht Frankfurt ta kasar Jamus, Oliver Glasner a matsayin sabon kocinta.
Wallafawa ranar:
Dan kasar Austria din mai shekaru 49 ya maye gurbin Roy Hodgson, wanda ya yi murabus a jiya Litinin don bai wa kungiyar damar ci gaba da shirinta na nada sabon mai horarwa a karshen wannan kaka.
Palace tana matsayi na 15 a teburin gasar Firimiya a yanzu haka, bayan da ta yi rashin nasara a wasanni 10 daga cikin 17 da ta buga a baya-bayan nan.
Glasner ya kulla yarjejeniyar zama a Palace har zuwa watan Yunin shekarar 2026, kuma shine zai jagoranci wasan da za ta buga da Burnley a gida a ranar Asabar mai zuwa.
Mataimakan Hodgson, Ray Lewington da Paddy McCarthy ne suka jagoranci wasan da Palace ta yi kunnen doki 1 da 1 a gidan Everton a daren Litinin, a yayin da Glasner, wanda bai kai ga nada mataimaka ba ya kalli wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu