Isa ga babban shafi

Firimiya ta sassauta hukuncin zaftare makin da ta yiwa Everton

Hukumar gudanarwar Firimiyar Ingila ta rage yawan makin da ta zaftarewa kungiyar kwallon kafa ta Everton daga maki 10 zuwa 6, lamarin da ya baiwa kungiyar damar farfadowa daga matakin na 17 a teburin gasar zuwa na 15.

'Yan wasan Everton.
'Yan wasan Everton. POOL/AFP
Talla

A watan Nuwamban bara ne mahukuntan na Firimiya suka zaftarewa Everton maki 10 bayan samunta da laifin karya dokokin kashe kudi wajen cinikayyar ‘yan wasa, matakin da a wancan lokaci ya dauki kungiyar daga matsayin da ta ke na 14 a teburin firimiya tare da mayar da ita ta 19.

Everton wadda tun da fari ta amsa tuhumar da ake mata, tuni ta yi maraba da sassaucin wanda zai kangeta daga tsintar kanta a ajin ‘yan dagaaji.

Duk da cewa akwai kuma wani tarnaki na daban da ke tunkaro Everton da ka iya kaiwa ga sake zaftare mata karin maki duk dai game da karya dokokin FA, amma matakin dawo mata da makin 4 a yanzu zai taimaka mata tsallake wannan kaka salin alin.

A ranar 8 ga watan Aprilu ne za a dawo da hukumar gudanarwar Firimiyar za ta koma ci gaba da sauraron tuhumar ta Everton, wanda ke nuna idan kungiyar ta daukaka kara zai kaita akalla ranar 24 ga watan Mayun gabanin ci gaba da sauraron tuhumar wato dai mako guda bayan kammala wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.