Isa ga babban shafi

PSG za ta rage amfani da Mbappe gabanin tafiya Real Madrid - Enrique

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta PSG Luis Enrique ya bayyana cewa ya zama wajibi tawagar ta fara koyon yadda za ta rika tunkarar wasanni ba tare da tauraronta Kylian Mbappe ba, bayan da aka ga yadda kocin ya sauya kyaftin din ana tsaka da wasan da kungiyar ta yi canjaras da Rennes jiya Lahadi a gasar Lig 1.

Dan wasan gaba na PSG da ke shirin komawa Real Madrid Kylian Mbappe.
Dan wasan gaba na PSG da ke shirin komawa Real Madrid Kylian Mbappe. AFP - MIGUEL MEDINA
Talla

A zantawarsa da manema labarai bayan wasan, Enrique ya ce rabuwa da Mbappe batu ne da babu tantama akansa, don haka dole tawagar ta koyi wasa babu shi walau a kusa ko a nesa.

Mbappe dan Faransa wanda ya zurawa PSG kwallaye 21 cikin wannan kaka, a sabuwar kakar cinikayyar ‘yan wasa ne zai koma Real Madrid, wato kungiyar da ya ke matukar so tun daga yarinta.

Kafin yanzu dai an yi ta kai ruwa rana game da  yiwuwar komawar dan wasan zuwa Spain, cinikin da ya gaza cimmuwa a kusan kakar wasa 3.

A cewar manajan na PSG akwai bukatar abokanan wasan Mbappe su yi amfani da damar barinsa Club din wajen nuna hazakarsu don samun madadinsa.

Yanzu haka dai PSG ke jagorancin teburin gasar da tazarar maki 11 bayan doka wasannin lig 18 ba tare da anyi nasara akanta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.