Kylian Mbappe ya amince ya koma Real Madrid a karshen wannan kaka
Dan wasan gaba na Paris St-Germain, Kylian Mbappe ya amince ya koma kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid a karshen wannan kaka da muke ciki.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tun da farko kyaftin din na tawagar kwallon kafar Faransa mai shekaru 25 ya shaida wa kungiyarsa cewa yana so su yi hannun riga da zarar kwantiraginsa ya kawo karshe a watan Yuni.
Mbappe bai kai ga sanya hannu a wata yarjejeniya da Real Madrid ba, amma za a sanar da cimma yarjejeniya da zarar an tabbatar da cewa kungiyoyin biyu ba za su kara da juna a gasar zakarun Turai na wannan kaka ba.
Dan wasan, wanda ya taba lashe kofin duniya, shine wanda ya fi kowa ci kwalllo a tarihin kungiyar ta PSG, inda yake da kwallaye 244.
Mbappe ya kudiri aniyar a warware batun makomarsa kafin watan Maris din nan, hakan ne ma ya sa a ranar 13 ga watan Fabrairu, jim kadan kafin atisaye ya tuntubi mai kungiyar PSG, Nasser Al-Khelaifi, kana ya shaida masa cewa zai bar kungiyar ya koma Real Madrid.
Kuma idan dan wasan tsakiya na kasar da Madrid, Luka Modric ya bar kungiyar a karshen wannan kaka, Mbappe ne zai gaji lamba 10 daga wajensa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu