Isa ga babban shafi
AFCON

Salah ya koma Liverpool don jinyar raunin da ya samu a gasar AFCON

Zakaran kwallon kafar Masar Mohamed Salah ya koma Ingila don samun kulawar likitoci karkashin kungiyarsa ta Liverpool bayan raunin da ya samu a gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Ivory Coast.

Belgium's midfielder Yannick Carrasco (L) and Egypt's forward Mohamed Salah vie for the ball during the friendly football match between Belgium and Egypt at the Jaber Al-Ahmad Stadium in Kuwait City
Dan wasan gaba na Masar da ke taka leda da Liverpool Mohamed Salah. © Yasser Al-Zayyat / AFP
Talla

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar da komawar Salah Anfield tun a jiya Lahadi don samun cikakkiyar kulawar.

Salah ya samu raunin ne a wasan da Masar ta yi canjaras da Ghana kwallo 2 da 2 ranar Alhamis, tawagar da yanzu haka ke matsayin ta biyu a rukuninta na B.

A yau litinin ne Masar ke shirin doka wasanta na 3 inda za ta hadu da Cape Verde, kuma dole sai ta yi nasara ne za ta iya tsallakawa matakin kasashe 16.

Tun a Juma’ar da ta gabata, hukumar kwallon kafar Masar ta bayyana cewa Salah ya samu rauni kuma ba zai sake haskawa a wasannin gasar ta cin kofin Afrika ba, face in kasar ta tsallakawa matakin wasan gab da na kusa da karshe da zai gudana a ranar 2 ko 3 ga watan Fabarairu.  

Da ake tambayar Jurgen Klopp kan ko Liverpool za ta baiwa Salah damar komawa gasar ta cin kofin Afrika, Manajan ya ce idan har Masar ta samu kaiwa wasan karshe kuma dan wasan ya murkure ko shakka babu zai koma Ivory Coast don doka wasan.

Wasu majiyoyi sun bayyana yiwuwar raunin na Salah ya iya tsananta fiye da hasashe lamarin da Jurgen Klopp ke cewa ya matukar fusata dan wasan wanda ke fatan lashe kofin karon farko.

Cikin fiye da kakar wasa 6, Salah na Masar wasanni 10 ne kadai bai iya dokawa Liverpool ba, duk da yadda ya ke jajircewa wajen wakiltar kasar shi.

Har zuwa yanzu dai Salah bai taba lashe kofin na cin kofin Afrika ba, domin kowa lokacin karshe da Masar ta lashe kofin shi ne shekarar 2010 shekara guda gabanin Salah ya fara doka wasanni a matakin kasa.

Sau 7 Masar na lashe kofin gasar a tarihi yayinda ta yi nasarar kaiwa wasan karshe a 2017 da 2021.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.