Masar ta tsallaka kwata final bayan doke Ivory Coast a gasar cin kofin Afrika
Masar ta fitar da Ivory Coast daga gasar cin kofin Afrika bayan doke ta a bugun fenariti da kwallaye 5 da 4 bayan da suka kammala mintuna 90 na wasan ba tare da kwallo ba haka zalika karin mintuna 30 da aka yi musu daga bisani.
Wallafawa ranar:
Mohammed Salah kaftin din tawagar ta Pharaohs ya zura kwallon karshe da ta bai wa kasar tasa nasara wadda ke da tarihin dage kofin gasar har sau 7 matsayin mafi dage kofin a nahiyar.
Yanzu haka dai Masar za ta hadu da Morocco ne a wasan kwata final ranar lahadi a filin wasa na birnin Yaounde.
Wasan na jiya dai ya zowa Bailly mai tsaron baya na Manchester United a wani yanayi duk da irin gagarumar gudunmawar da ya bayar a wasan don ganin kasarsa Ivory Coast ta yi nasara amma kuma shi ne dan wasa daya daya gaza zura kwallo a bugun fenaritin.
Ivory Coast din dai ita ta fitar da Algeria mai rike da kambun gasar bayan lallasa ta a wasansu na karshe matakin rukuni.
Yayin wasan na jiya dan wasan Masar Mohamed El Shenawy ya samu rauni a kafa wanda ke nuna babu tabbacin ya iya kasancewa cikin tawagar da za ta kara da Morocco a karshen mako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu