Isa ga babban shafi

Mun shiryawa yakin nukiliya matukar Amurka ta girke dakaru a Ukraine- Putin

Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa Rasha ta shiryawa yakin Nukiliya tsakaninta da Amurka matukar Washington ta yi kuskuren tura dakaru Ukraine yana mai ikirarin cewa Moscow na da makaman nukiliya fiye da Amurka da ma kowacce kasa a Duniya.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha. via REUTERS - POOL
Talla

A jawabinsa gabanin babban zaben Rasha na ranakun 15 zuwa 17 ga watan nan da zai sake baiwa jagoran damar ci gaba da jan ragamar kasar na tsawon shekaru 6 a nan gaba, Putin ya sake aikewa da gargadi ga kasashen yammaci musamman Amurka game da yunkurinsu na aikewa da dakaru Ukraine, yana mai cewa kai tsaye matakin zai bude kofa ga yakin nukiliya.

A cewar Putin babu bukatar amfani da makaman nukiliya kan Ukraine a yanzu, sai dai shigar dakarun ketare da kuma amfani da muggan makamai kan Rasha, kai tsaye zai bude kofa ga yakin nukiliyar.

Putin mai shekaru 71 da ya ke amsa tambaya kan ko Rasha a shirye ta ke ga yakin na Nukiliya, shugaban na Moscow ya bayyana cewa ko shakka babu ta fuskar karfin soji da kere-kere Rasha a shirye ta ke ga kowanne nau’in yaki ciki har da na nukiliyar.

Vladimir Putin ya nanata cewa akwai bukatar Amurka ta sani cewa duk wani yunkuri na girke dakaru a Ukraine kai tsaye matakin na nufin tokalar yaki ne tsakanin kasashen biyu.

A cewar Putin baya tunanin nan kusa akwai wani dalili da ya zai sanya kasashen na Amurka da Rasha mafiya karfin nukiliya su tsunduma yaki, said ai idan hakan ya faru Moscow a shirye ta ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.