Isa ga babban shafi

Rasha ta yi gwajin harba makami mai linzami mai karfin nukiliya

A yau lahadi Rasha ta ce ta yi nasarar harba wani makami mai linzami da ke iya daukar makamin nukiliya da ya ratsa nahiyoyi daga daya daga cikin jiragenta na karkashin ruwa.

Vladimir Poutine Shugaban Rasha yayin taron  Valdaï,a Rasha
Vladimir Poutine Shugaban Rasha yayin taron Valdaï,a Rasha AP - Grigory Sysoyev
Talla

Harba makami mai linzamin na "Bulava", wanda shi ne na farko cikin sama da shekara guda, ya zo ne a daidai lokacin da kasar Rasha ke kara yin tsokaci kan batun nukiliyar tun bayan da ta soke amincewa da wata muhimmiyar yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce ta harba makami mai linzamin da ke karkashin teku daga wani wuri da ba a bayyana ba a cikin tekun White Sea da ke gabar tekun arewa maso yammacin kasar, zuwa wani yanki dake dubban kilomita daga yankin gabashin Kamchatka mai nisa.

Rasha ta gwajin makamin nukiliya
Rasha ta gwajin makamin nukiliya © RFI

"An harba makami mai linzamin ne a yanayin da aka saba daga wani wuri karkashin ruwa.

Makamin Bulava mai tsayin mita 12 an kera shi ne domin ya zama kashin bayan nukiliyar Moscow kuma yana da nisan sama da kilomita 8,000 (kusan mil 5,000).

Kasashen Yamma sun zargi Moscow da yin amfani da kalaman Nukiliya na rikon kwarya tun bayan da ta kaddamar da farmaki kan Ukraine a watan Fabrairun da ya gabata.

Karfin soja na Rasha
Karfin soja na Rasha AP - Gavriil Grigorov

A farkon makon nan ne shugaban kasar Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ta soke amincewar da kasar Rasha ta yi kan yarjejeniyar hana gwajin makamin nukiliya, matakin da Amurka ta yi kakkausar suka.

Yarjejeniyar 1996 ta haramta duk wani fashewar makaman nukiliya, ciki har da gwaje-gwajen makaman nukiliya kai tsaye, duk da cewa ba ta fara aiki ba saboda wasu muhimman kasashe - ciki har da Amurka da China, ba su taba amincewa da ita ba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.