Isa ga babban shafi
Yakin Gaza

Hamas ta ce Isra'ila ta kashe mutane sama da dubu 7 a Gaza

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa, sama da  mutanen Gaza dubu 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren Isra'ila tun daga ranar 7 ga watan nan na Oktoba, yayin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya sake gaza daukar mataki kan rikicin na  Isra'ila da Hamas duk da matsalolin jin kai da ke kara tsananta a yankin Zirin Gaza na Falasdinawa. 

Dubban rukunan gidaje ne suka rushe a yayin hare-haren Isra'ila a Gaza
Dubban rukunan gidaje ne suka rushe a yayin hare-haren Isra'ila a Gaza AP - Hatem Ali
Talla

A ranar Laraba ne kasashen Rasha da China suka ki amincewa da kudurin da Amurka ta gabatar saboda rashin gamsuwarsu da kudirin wanda ya bukaci tsagaita wuta domin bayar da damar kai kayan agaji cikin Gaza na wani dan lokaci.

Kudirin ya kuma kunshi kare fararen hula da kuma dakatar da bai wa kungiyar Hamas da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai a Zirin Gaza makamai. 

Rasha da China sun yi fatali da wannan kudiri ne saboda babu wata manufa da yake dauke da ita ta hana Isra’ila ci gaba da kisan bayin- Allah a Gaza.

Tuni Rasha ta gabatar da ita ma nata kudirin, amma ya gaza samun isassun magoya baya da za su mara mata.

Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada goyon bayansa da Isra'ila a yakin da take yi da Hamas a Zirin Gaza.
Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada goyon bayansa da Isra'ila a yakin da take yi da Hamas a Zirin Gaza. AP - Evan Vucci

Amurka ta yi watsi da daftarin farko da aka gabatar a karshen mako bayan da jami'an diflomasiyya suka bayyana kaduwarta game da gazawarta wajen shawo kan yadda lamarin ke shafan fararen hula, da kuma tsayawa kai da fata da Amurkar ta yi na cewa Isra'ila na da 'yancin kare kan ta. 

Mambobi 10 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin, yayin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta ki amincewa, sannan Brazil da Mozambique suka kaurace. 

Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza

Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta na kasa sun kutsa cikin arewacin Zirin Gaza cikin dare tare da tankunan yaki, inda suka kai farmaki kan cibiyoyin da suke zargin na mayakan Hamas inda kuma daga nan suke harba wa Isra’ila makaman roka. 

Daga bangaren Lebanon kuwa, bayanai sun ce da yammacin jiya Laraba jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a wasu sassan kasar a matsayin ramuwar gayya kan harba mata makamai masu linzami da mayakan Hezbollah ke yi.  

Karancin shigar da kayan agaji zuwa Gaza  

Har yanzu dai Isra'ila na ci gaba da katse samar da ruwan sha da abinci da sauran kayayyakin bukata ga Zirin Gaza, yayin da ya zuwa yanzu motocin agaji kasa da 70 kadai ne suka shiga yankin na Gaza. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an rufe asibitoci 12 daga cikin 35 da ke Zirin na Gaza saboda rusa su da Isra’illa ta yi yayin hare-haren da take ci gaba da kaiwa, ko kuma saboda rashin man fetur, yayin da Hukumar Kula da Falasdinawa ‘Yan gudun hijira ta ce tuni ta dauki matakin rage ayyukanta, domin kuwa  fiye da kashi 90 cikin 100 na abinci da  magunguna da sauran muhimman kayayyaki sun kare. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.