Rasha na shirin tattauna batun soke yarjejeniyar hana gwajin makamin Nukiliya
Kasar Rasha na shirin tattauna batun soke amincewa da yarjejeniyar hana gwajin makamin Nukiliya, kamar yadda kakakin majalisar dokokin kasar ya fada a yau Juma’a. Vyacheslav Volodin ya bayyana hakan ne kwana guda bayan da shugaban kasar Vladimir Putin ya bayyana yiwuwar daukar wannan mataki, wanda zai iya kara dagula al'amura a tsakanin Rasha da kasashen Yamma.
Wallafawa ranar:
Wannan al’amari na Rasha na zuwa ne a daidai lokacin da Moscow ke kaddamar da hare-haren soji a Ukraine.
Rasha a taron majalisar kasar na Duma za a tattauna batun soke amincewa da yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya," in ji Volodin a cikin wata sanarwa.
Hakan zai zama martani ga Amurka wacce har yanzu ba ta amince da yarjejeniyar ba da kuma ke bayar da taimako ga kasar Ukraine a wannan yaki da Rasha.
A shekara ta 2000 ne Rasha ta amince da yarjejeniyar. Washington ta ba da sanarwar dakatar da gwaje-gwaje a cikin 1992 kuma a cikin 1996 ta sanya hannu kan yarjejeniyar haramcin gwajin amma har yanzu ba ta amince da ita ba.
Rasha daga Shugaban kasar Putin,‘‘yana yiwuwa a soke amincewa, kuma idan muka yi hakan, zai wadatar."
Shugaban na Rash ana fadar hakan ne a wani taron kungiyar Tattaunawa ta Valdai a jiya Alhamis.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu