Isa ga babban shafi

Ukraine ta soki matakin bai wa Rasha damar dawowa cikin wasannin Turai

Hukumar kwallon kafar Ukraine ta yi barazanar cewa za ta kauracewa dukkanin wata gasa karkashin UEFA da aka bai wa Rasha damar komawa cikinta.

Tun farko Uefa da kanta ta nemi ganin tawagar ta Rasha 'yan kasa da shekaru 17 sun samu damar taka leda a wasannin na Turai.
Tun farko Uefa da kanta ta nemi ganin tawagar ta Rasha 'yan kasa da shekaru 17 sun samu damar taka leda a wasannin na Turai. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

A jiya talata ne Uefa ta sanar da cewa tawagar kwallon kafar Rasha ta ‘yan kasa da shekaru 17 za ta iya fafatawa a gasar nahiyar bayan dakatarwar watanni 19 da aka yi wa kasar tun bayan da ta kaddamar da mamaya kan Ukraine.

Sai dai a wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Ukraine ta fitar yau laraba, ta ce ko shakka babu idan har Uefa ta amince da dawowar tawagar Rasha cikin wasannin nahiyar kai tsaye ita za ta fice daga ciki.

Sanarwar ta roki Uefa da kada ta amince da matakin dawowar tawagar ta Rasha cikin dukkanin gasar Turai.

Kwamitin zartaswar hukumar ta Uefa ne ya mika bukatar ganin an dawo da kasar ta Rasha cikin gasar ta cin kofin nahiyar Turai ta ‘yan kasa da shekaru 17 bisa sharadin cewa babu kowanne wasa da zai gudana cikin Rasha haka zalika babu dan wasan da zai sanya rigar Rasha ko kuma daga tutar kasar.

Wasan karshe na gasar zakarun Nahiyar ta Turai dai zai gudana ne a Cyprus badi haka zalika ta bangaren mata a Sweden cikin watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.