Faransa za ta takaita zirga-zirgar ababen hawa a Paris
Hukumomin kasar Faransa sun sanar da daukar matakin takaita zirga-zirgar ababen hawa domin rage cinkoso a Paris, babban birnin kasar
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Wannan matakin na zuwa ne, domin rage gurbatar yanayi a faransa, kamar yadda Anne Hidalgo, magajiyar garin Paris ta sanar.
Matakin zai takaita Cunkoson ababan hawa, da zai rage hayakin da su ke fitar wa wanda ke matukar yin illa ga lafiyar al’umma.
Wannan dai, bashi ne karo na farko ba, da hukumomin kasar faransa ke daukar wannan matakin, yayinda a bara, an dau irin wannan matakin, saboda matsanancin sanyi cikin dare,da zafi da rana, dake hana hayakin motoci bajewa, tare da haddasa gurbatar yanayin.
A makon daya gabata, gurbatar yanayi a faransa, ya kai wani mizani daya zarce na biranen New Delhi da Beijing, inda suma ke fama da irin wannan matsalar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu