Isa ga babban shafi
Faransa-EU

Faransa ta yi alkawarin mutunta ka'idojin kungiyar EU

Fraiministan kasar Faransa Manuel Valls ya ce, kasar zata mutunta duk wasu ka’idodi da kungiyar Tarayyar Turai, EU ta shimfida mata, wajen daidaita kasafin kudin kasar, amma zata kaucewa duk wani mataki da zai jawowa tattalin arzikinta koma baya. Duk da adawar da wasu daga cikin kasashe 28 mambobin kungiyar ta EU suka nuna kungiyar, Tarayar Turai ta baiwa Faransa daga nan zuwa shekarar 2017 da ta mai da gibin kasafin kudin da take fuskanta da kashi 3 cikin dari. A lokacin da ya ziyarci hukumar gudanarwar kungiyar ta Tarayyar Turai dake birnin Bruxelles a jiya talata PM kasar ta Fransa Manuel Vallas ya bayyana cewa duk wani mataki bunkasa tattalin arziki in dai har zai iya jawowa ci gaban tattalin arzikin kasar ta Faransa cikas, to doli ne su yi taka tsantsan da shi.A wani taron manema labarai na hadin guiwa tare da shugaban komitin gudanarwar kungiyar ta Tarayyar Turai Jean Claude Junker, a jiya, Mr Valls ya kara da cewa ba zai taba aiki da duk wata hanya da zata yi hannun riga da manufofi ko tsarin ci gaban kasar Faransa ba, haka ita kanta gomnatinsa ba zata taba aiki da shi ba.Idan dai ba a manta ba kungiyar ta EU ta baiwa Faransa karin wa’adin shekaru 2 nan gaba, da ta kokarta ganin ta rage gibin kasafin kudin da take fama da shi zuwa kashi 3 cikin dari, matakin da wasu kasashen na Turai ke kallon a matsayin nuna banbanci tsakanin kasashen da kungiyar ta yi, ta wajen baiwa Faransar wannan dama sabanin wasu kasashen da basu samu hakan ba. 

Fraiministan Faransa Manuel Valls
Fraiministan Faransa Manuel Valls AFP PHOTO / DAMIEN MEYER
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.