Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

Rasha ta cafke wata ‘Yan kasar Ukraine

Jami’an tsaron Rasha sun kama wata ‘Yar kasar Ukraine, da ke aikin Jirgin sama da ake tuhuma akan mutuwar wasu ‘yan Jaridan kasar guda biyu. Masu bincike a kasar Rasha sun ce sun kama matar mai tukin jirgin sama, mai suna Nadiya Savchenko, da ke cikin mata tsirarun da ke aiki a rundunar sojan saman kasar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Talla

Ana zarginta da hannu a abinda Rasha ta kira kisan ‘yan jaridan da gangan, yayin fadan da aka yi a gabashin kasar, a watan daya gabata.

Sai dai tuni hukumomin kasar Ukraine suka yi Allah wadai da wannan matakin.

A ranar 18 ga watan Yuni ne Igor Kornelyuk da Anton Voloshin, masu aiki a gidan talibijin din Rossiya, mallakin gwamnatin kasar Rasha, suka mutu bayan burbushin makaman da dakarun Ukraine suka harbo ya same su.

Hukumomin birnin Kiev sun ce makaman sun sami ‘yan jaridun ne, sakamakon rashin sanya rigunan kariya, amma kuma Rasha tace da gangan aka auna makaman, bayan ta gudanar da bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.