Isa ga babban shafi
Thailand

Sojoji sun rusa Majalisar Dattawan kasar Thailand

Babban kwamandan sojojin Thailand wanda ya jagoranci juyi mulki a kasar Janar Chan O-Chan, a yau asabar ya sanar da rusa majalisar dattawan kasar tare da mayar da illahirin ikon zartaswa a hannun sojojin kasar.

Masu adawa da juyin mulkin kasar Thailand
Masu adawa da juyin mulkin kasar Thailand REUTERS/Damir Sagolj
Talla

Har ila yau rundanar sojan ta tabbatar da cewa yanzu haka tubabbiyar Firaminsitar kasar Yingluck Shinawatra da wasu manyan jami’an gwamnatinta na tsare a hannunsu.

To sai dai yanzu haka dubbaun mutane ne ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojojin suka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.