Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan Jaridun Faransa da suka tsira a Syria sun isa gida

‘Yan jaridun kasar Faransa hudu da aka sako bayan garkuwa da su da aka yi a kasar Syria, na tsawon watanni goma sun isa gida, inda suka samu tarbo daga iyalansu da kuma shugaban kasa Francois Hollande.

‘Yan Jaridun Faransa da suka tsira a Syria sun isa gida
‘Yan Jaridun Faransa da suka tsira a Syria sun isa gida REUTERS
Talla

Cike da murna a kuma wani yanayi mai sosa rai, kafofin yada labarai na talebijin sun nuna ‘yan jaridun suna rungumar iyalansu, da kuma abokanan aikinsu, bayan da suka sauka a wani filin tashi da saukar jirage na soji da ke kudancin birnin Paris.

Dukkaninsu akwai alamun gajiya a tattare da su kamar yadda hoton bidiyon ya nuna, hade da cewa sun rame daga wahalhalun da suka sha, a lokacin da suna tsare.

Baya ga iyalansu, shugaba Francois Hollande shi ma yana cikin wadanda suka tarbi ‘yan jaridun, tare da gaisawa da dukkaninsu, da bayyana cewa wannan rana ce ta farin ciki ga Faransa.

An dai yi garkuwa ne da ‘yan jaridun su hudu yayin da suke dauko rahotanni a kasar Syria a watan Yulin bara, sun kuma hada da Didier Francois dan shekaru 53 da Eduard Elias dan shekaru 23 da Pierre Torres dan shekaru 29 da kuma Nicolas Henin dan shekaru 37.

Gwamnatin Faransa dai ta ce bata biya kudin fansa ba kamin a sako su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.