Isa ga babban shafi
Mali

An cafke mutane 10 akan kisan ‘Yan Jaridun RFI

Hukumomi a kasar Mali, sun sanar da cafke mutane fiye da 10, da ake zargi da hannu wajen kashe wakilan gidan Rediyo Faransa guda biyu Ghislaine Dupont da Claude Verlon a garin Kidal, , yayin da ita kuma gwamnatin Faransa ta bayyana cewa sojojin kasar za su ci gaba da kasancewa a Mali domin yaki da ayyukan ta'addanci.

Shugabannin Rediyo Faransa suna ganawa da Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita bayan kisan Jan Jarida a Kidal
Shugabannin Rediyo Faransa suna ganawa da Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita bayan kisan Jan Jarida a Kidal AFP PHOTO/HABIBOU KOUYATE
Talla

Kakakin gwamnatin kasar Faransa Najat Vallaud Belkacem, ta ce yanzu haka dakarun Faransa, da na Majalisar Dinkin Duniya da Sojojin Afirka da dakarun Mali, na kan aiki tukuru domin gano wadanda ke da hannu wajen kashe 'Yan jaridun biyu, yayin da majiyoyin 'Yan sanda a garin Gao ke cewa an cafke mutane fiye da 10 da ake zargin suna da hannu a lamarin.

Sai dai duk da faruwar wannan lamari kamar yadda Belkacem ta ci gaba da cewa, sojojin Faransa da yawansu ya haura dubu uku, za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na wanzar da tsaro, da yaki da 'yan bindiga a cikin Mali, tana mai cewa ai dama aikin yaki da ta'addancin abu ne da ke bukatar lokacin kafin samun nasararsa.

A birnin Bamako, Shuganban kasar Mali Ibrahim Boubakar Keita, wanda ke ganawa da wata tawagar hukumar gudanarwa ta gidan Rediyo Faransa RFI, ya ce yanzu haka bangaren shari'a a kasar da na kasar Farasnsa na aiki tukuru domin gano masu hannu a lamarin.

Shugaba Keita ya ce shi kansa da kuma al'ummar kasar Mali, sun damu matuka sakamakon faruwar wannan kisa da aka yi wa Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon a kusa da garin Kidal mai tazarar kilomita dubu daya da dari biyar daga Bamako a ranar Assabar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.