Isa ga babban shafi
MDD-Mali

Ban Ki moon zai fara ziyarar wasu kasashen Afrika ta Yamma

Yau ake sa ran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki moon, zai fara ziyarar aikin wasu kasashen Afrika ta Yamma, inda ake sa ran zai je Mali, Jamhuriyar Niger, Burkina Faso da kuma Chadi. 

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki moon
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban ki moon
Talla

Yau ake sa ran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki moon, zai fara ziyarar aikin wasu kasashen Afrika ta Yamma, inda ake sa ran zai je Mali, Jamhuriyar Niger, Burkina Faso da kuma Chadi.

Ita dai wannan ziyara da Ban Ki moon zai fara yau, ana sa ran ta bashi dama dan ganewa idonsa ci gaban da aka samu wajen mayar da kasar turbar demokradiya da kuma yaki da ake da ‘Yan Tawayen dake dauke da makamai a Arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da amfani da karfi wajen murkushe ‘Yan Tawayen dake dauke da makamai a Mali, bayan hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure da sojoji suka yi, abinda ya haifar da matsalar ‘Yan Tawaye a cikin kasar.

Har ila yau, Ban zai je Jamhuriyar Niger, inda ake sa ran zai yabawa hukumomin kasar kan gudumawar da suka bayar wajen tallafawa kasar Mali da ‘Yan gudun hijirar kasar, kafin ya zarce zuwa Burkina Faso da Chadi dan ganawa da shugabanin kasashen biyu, wadanda suma suka yi ruwa da tsaki a sasanta rikicin na Mali.
 
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.