Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta kaddamar da yaki akan ‘Yan a ware

Kasar Ukraine ta aika da sojoji a yankin gabacin kasar domin tunkarar “ ‘Yan a ware” masu ra’ayin Rasha da suka karbe ikon gine ginen gwamnati.Tuni Rasha ta yi gargadin cewa Ukraine ta kama hanyar fadawa Yakin basasa.

Yan a ware da suka karbe ikon gine-gine gwamnatin a gabacin Ukraine
Yan a ware da suka karbe ikon gine-gine gwamnatin a gabacin Ukraine REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Sa’o’I ashirin da biyu bayan wa’adin da gwamnatin Ukraine ta ba ‘yan a waren su mika makwamansu ya kawo karshe, rahotanni daga Ukraine din na cewa akwai dakaru na musamman da suka kama hanya zuwa yankin Slavyansk da ke gabacin kasar domin tunkarar ‘Yan tawayen da suka karbe ikon gine ginen gwamnati.

Tuni Gwamnatin Ukraine tace zata kaddamar da yaki da ‘yan ta’adda. Kuma yanzu haka rahotanni na cewa akwai jerin gwanon tankokin yaki da ke kan hanyarsu zuwa Donetsk don fatattakar ‘yan tawayen masu ra’ayin komawa ikon Rasha.

Akwai dai taro na musamman da ake shirin gudanarwa a Geneva tsakanin Rasha da Amurka da Kungiyar Turai domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin na Ukraine da ake ganin ya kazance.

‘Yan a waren masu dauke da makamai sun karbe ikon ofisoshin ‘yan sanda ne kusan a birane 10 da ke gabacin Ukraine, wadanda ke naman ballewa daga kasar kamar yadda ta faru da Crimea.

To tambaya dai anan shin ko ya Rasha za ta karbi mutanen yankin na gabaci, wadanne matakai ne kuma kasashen Turai da Ukraine zasu dauka bayan sun kakabawa Manyan Jami’an Rasha Takunkumi?

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.