‘Yan Majalisun Macedonia sun ba hamata iska game da kasafin kudin shekara
An samu sabani a Majalisar Macedonia inda aka bai wa hammata iska tsaknin ‘Yayan jama’iyya mai mulki da ‘Yan adawa, a majalisar dokokin kasar. Rikicin ya barke ne sakamakon muhawarar da ake yi akan kasafin kudin shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar:
A daya bangaren kuma magoya bayan jama’iyyun da ke adawa da juna sun yi ta jifar junansu da duwatsu da kwalabe a harabar majalisar.
Dubun dubatar masu zanga zanga ne suka nufi majalisar, bayan magoya bayan jama’iyyar adawa ta ‘yan gurguzu, sun killace harabar majalisar, don nuna adawa da shirin amincewa da kasafin kudin, da suka ce zai sa a yi ta kashe kudaden gwamnati ba kakkautawa.
‘Yan Majalisa biyu ne dai suka samu rauni sanadiyyar rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu