Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojan Nijar ta rusa majalisun kananan hukumomin kasar

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta rusa dukan majalisun kananan hukumomi na jiha da manyan birane  a fadin kasar tare da maye gurbinsu da kantomomi.

Jagoran mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani.
Jagoran mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani. © Balima Boureima / Reuters
Talla

A wata sanarwa da shugaban mulkin sojan kasar ya rattabawa hannu da aka karanta da gidan talbijin na kasar ya bayyana cewa an dauki matakin ne bisa kokarin wasu gyare-gyare.

Wadanda aka korar dai yawancinsu zababbu ne a tsohuwar gwamnati da suka share watanni 8 suna jan zarensu, tun bayan hanasu taba kudaden da’irorinsu a makon jiya akayi hasashen korarsu daga mukaman.

Tun a baya dai ‘Yan kungiyoyin fararen hula sun yi ta caccakar sojojin da cewa sun yi juyin mulki amma sun bar magajan gari kan mukamansu abin da ga al'ada ba a taba gani ba.

A ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023 ne sojojin suka kifar da gwamnatin dimokaradiyyar kasar, karkashin jagorancin shugaba Bazoum Muhammane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.