Isa ga babban shafi

Dubban 'yan Nijar sun gudanar da zanga-zangar neman ficewar sojojin Faransa

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga yau asabar a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar domin bukatar Faransa ta janye sojojinta kamar yadda gwamnatin mulkin sojan da ta kwace mulki a watan Yuni ta bukaci ta yi.

Wasu masu zanga-zangar neman ficewar dakarun Faransa a Nijar. a Niamey, 30/08/2023
Wasu masu zanga-zangar neman ficewar dakarun Faransa a Nijar. a Niamey, 30/08/2023 © REUTERS - Mahamadou Hamidou
Talla

Masu zanga-zangar dai sun taru ne a kusa da wani sansani dake dauke da sojojin Faransa, biyo bayan kiran da wasu kungiyoyin fararen hula da ke adawa da kasancewar sojojin Faransa a kasar da ke yammacin Afirka suka yi.

Masu zanga-zangar na dauke da allunan da aka rubuta cewa "Rundunar sojojin Faransa ko fice daga kasarmu".

A ranar Juma'ar da ta gabata ne sojoji da suka yi juyin mulki suka kaddamar da sabon takun-tsaka da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, bayan da suka zarge ta katsalandan a fili ta hanyar mara wa hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum baya, yayin da masu zanga-zangar suka gudanar da makamaicin gangami a kusa da wani sansanin Faransa da ke wajen birnin Yamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.