Isa ga babban shafi
kungiyar tarayyar turai

EU za ta dau mataki kan matsalar Bakin haure

Babbar Jami’ar Diflomasiyar Turai Federica Mogherini tace a yanzu ba su da zabi illa su gaggauta daukar mataki game da matsalar bakin haure da ke mutuwa a tekun Mediterranean a yayin da suke kokarin tsallakawa zuwa Turai  

Jami'an kiwon lafiya na duba lafiyar bakin hauren da suka Isa Kasar Italiya a Jirgin ruwa
Jami'an kiwon lafiya na duba lafiyar bakin hauren da suka Isa Kasar Italiya a Jirgin ruwa REUTERS/Stringer
Talla

An dade dai ana sukar kungiyar Turai na rashin damuwa da matsalar bakin hauren da ke mutuwa kusan a kullum a lokacin da suke kokarin tsallaka wa Turai, inda kwale kwalen da ya kwaso su ke kife wa dasu a Teku.

A bana an kiyasata cewa kimanin bakin haure sama da 1,000 ne suka mutu.

Hukumomin ‘yan gudun hijira da kungiyoyoin kare hakkin bil’adama sun bukaci kungiyar Tarayyar Turai ta gaggauta inganta matakan da suka dace na ceto bakin haure, tare da gano dalilin da yasa bakin hauren ke tsallakwa zuwa Turai.

A bangare guda, hukumomin Italiya da ke fama da bakin hauren sun ce kimanin mutane 11,000 suka ceto a cikin makon jiya kawai. Kuma sun bayyana fargaba akan adadin mutanen da ke kokarin tsallakowa zuwa Turai na iya zarce na bara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.