Isa ga babban shafi
Girka

EU ta ba Girka wa’adi zuwa 20 ga Afrilu

Kungiyar Kasashen Turai ta bai wa kasar Girka wa’adin zuwa ranar 20 ga watan Afrilu don ta gabatar da shirin sauye sauyenta wanda zai kai ga cire takunkumin ba ta tallafin biliyoyin euro. Kungiyar ta sanya wa’adin ne don ba Girka damar nazarin shirin kafin taron da za ta gudanar a ranar 24 ga watan Afrilu.

Firaministan kasar  Girka Alexis Tsipras
Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras Reuters/Alkis Konstantinidis
Talla

Wakilan Girka da kungiyar kasashen Turai na cigaba da tafka muhawara kan yadda kasar ta ki amincewa ta rage fanshon ma’aikata domin karbar tallafin euro biliyan sama da 7.

Tuni dai Girka ta yi alkawalin biyan bashin da asusun bayar lamuni ke bin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.