Isa ga babban shafi
Girka

Girka ta tada tsohon bashin da take bin Jamus

Yayin da masana ke ganin watakila kasar Girka dake fama da matsalolin tattalin arziki ta fice daga kungiyar kasashen Turai, a yanzu haka kasar ta taso da tsohon bashi da take bin kasar Jamus tun lokacin yakin duniya na biyu

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Markel da Firaministan Girka, Alexis Tsipras
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Markel da Firaministan Girka, Alexis Tsipras REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Wannan tsohon bashin, kasar Girka tace tana bin kasar Jamus ne na kudin fansa saboda mamayar da Nazi sukayi a lokacin yakin duniya na biyu.

Wannan tada tsohon bashin, na zuwa ne saura kwanaki kadan wa’adi ya cika na Girka tayi aman kudaden da suka kai Dalar Amurka miliyan 487, biyan bashi ga asusun bada lamuni na duniya.

Gwanayen kididdigan kudi dake Girka, sun gabatar da alkaluman bashin karo na farko da suka ce suna bin kasar Jamus, da ya kai Dalar Amurka biliyan 302 dake nuna yawan bashin har ya zarce bashin kudin da Kungiyar Turai da Asusun bada lamuni na duniya ke bin Girka.

Sai dai kuma Jamus tace wancan bashin saboda batun mamayar Nazi ta biyashi, amma kuma Girka tace biyan wani kaso ne kadan aka yi a shekara ta 1960.

Babu dai wasu gamsassun bayanai ko Girka na da hurumin samun wadannan kudade, amma kuma wannan tada tsohon bashin na kara nunawa karara cewa Girka, idanta a rufe su ke.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.