Isa ga babban shafi
Tunisia

Masu yawon bude ido sun mutu a harin gidan tarihin Tunisia

kimanin Baki daga kasashen ketare 17 ne, suka rasa rayukansu, sakamakon wani harin ta'addacin da aka kaddamar a wani gidan tarihin Bardo dake birnin Tunis na Kasar tunisia.

Shugaban Kasar Tunisia, Caid Essebsi
Shugaban Kasar Tunisia, Caid Essebsi AFP PHOTO / FETHI BELAID
Talla

Mai Magana da yawun Ministan cikin gidan kasar Tunisia Muhammed Ali Aroui ya shaidawa taron manema labarai cewa, wadanda suka kai harin na iya zarce mutane 2, kuma sun hallaka mutane 19 daya hada da ‘Yan asalin Kasar biyu, baya ga 22 da suka jikkata.

Ali Aroui yace sama da yan yawon bude ido 100 ne ke cikin gidan tarihi Bardo, yanzu haka ana kyautata zaton yan bindigan sun yi garkuwa da wasu masu yawon buda idon sai dai kuma ba’a tattance adadin su ba.

Tuni dai jam’ian tsaro kasar suka yi wa gidan tarihin na bardo kawanya, kuma harin nazuwa ne, a lokacin da shugaban kasar Beij Caid Essebsi ke shirin gabatar da wani jawabi na musamman ga al’umma kasar.
Tuni dai kasar faransa ta yi tayi la’anci wannan harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.